Matsalolin tsaro na kara kamari a Najeriya
February 20, 2020Talla
A Najeriya matsalolin tsaro na kara kamari a yankunan da dama na kasar musamman na yankin arewacin kasar inda 'yan Boko Haram da kuma 'yan bindiga ke ci gaba da daukar rayukan jama'a. Sai dai kuma duk da kamari da yanayin tabarbarewar tsaron ke yi, gwamnatin kasar ta ce ba ta da niyyar sauya hafsoshin sojan kasar, wannan kuwa duk da kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar da kuma musamman 'yan majalisa ke yi na ganin an sauya hafoshin tsaron kasar domin dora sabbin jini da za su fi tunkarar matsalolin na tsaro a fadin kasar.