1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Matsalolin yaki da cutar AIDS

December 1, 2025

A lokacin ake bikin ranar yaki da cutar HIV/AIDs ko SIDA ta duniya daya ga watan Disamba kowace shekara ana samun barazanar karuwar cutar tsakanin al'umma sakamakon karancin kayan gwaje-gwaje da magunguna.

Alamun yaki da cutar AIDS
Alamun yaki da cutar AIDSHoto: Sylvain Grandadam/IMAGO

 

Kasashe da dama a duniya na shan radadin janye tallfin USAID a karkashin gwamnatin shugaba Amurka Donald Trump.

Yaki da cutar AID na fuskantar matsaloli a kasashe masu tasowa musamman na Afirka, sakamakon matakin Amurka na janye tallafi, kamar abin da ake gani a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Masana lafiya da sun nunar da irin matsalolin da ake fuskanta na kayan aiki bayan janye tallafin da Amurka ta yi.

Haka labarin yake a Jamhuriyar Nijar

Kororon roba na wayar da kai game da yaki da cutar AIDSHoto: TONY KARUMBA/AFP/Getty Images

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar kasa da kasa ta yaki da cutar Sida sai dai kimanin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata kusan komai ya tsaya game da ayyukan yaki da cutar musaman ayyukan waye kai sai kwatsam kasar Amurka ta bayana janye tallafin da take yi lamarin da masu nazarin al'amura ke ganin zai kara jefa rayuwar masu dauke da cutar cikin wani hadari.

A fili yake yaki da cutar Sida/AIDS na fuskantar matsaloli da barazana iri-iri sakamakon janyewar tallafi daga kungiyoyi agaji na duniya. Yanzu haka masu dauke da cutar na cikin  matsaloli Madame Rakiya Mahaman daya daga cikin mata masu dauke da cutar kimanin shekaru 20 ta bayana halin da suka samu kansu na kunci bayan matakin janye tallafin na MAurka, inda take cewa yanzu ba su da madogara.

A Ghana ma haka lamarin yake

Kwaji kan cutar AIDSHoto: Jeremy Jowell/IMAGO

A watan Febarairun shekarar nan ta 2025 mai karewa ne sShugaba Donald Trump Amurka ya katse taimakon kasashen duniya, lamarin da ya shafi fannin kiwon lafiya na masu dauke da cutar AIDS a kasar ta Ghana.

Ghana da wasu kasashen Afrika da ke dogaro da tallfin, sun fara lalubo hanyoyin fidda wa kansu kitse a wuta kazalika da samar hanyoyin cike basusukan da matakin ke nufi ga gwamnati bayan katsewar tallafin na sama da shekaru 60.

 

 

Yaki da cutar AIDSHoto: JOE KLAMAR/AFP/Getty Images

A wannan shekarar kadai Ghana ta nemi tallafin dalan Amurka miliyan 138.7 da muradin karfafa bangarori daban-daban na kiwon lafiya a kasar, wanda yanzu ga duk alamu ke nuni da cewa wajibi ne Ghana ta waiwayi wasu dubarun tattara kudin wanda ya kumshi tattara kudade a cikin gida, ko kuwa hadin gwaiwa da wasu abokan tallafin na kasa da kasa da ma bangarorin masu zaman kansu.

Inda masana ke ganin Tarayyar Turai, bankin duniya ko kuwa asusun lamunin kudi na, IMF, za su iya yin tasiri wajen cike gibin da USAID ta bari duk da cewa ba lallai ne tallafi daga wadannan jerin kungiyoyin su iya cike gibin baki dayansa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani