Habasha: 'Yan Tigray na ci gaba da tagaiyara
January 21, 2025Yarjejeniyar Afrika ta Kudu da aka rattaba hannu kan bukatar tsagaita bude wuta tsakanin gwamantin Habasha da mayakan Tigray ta kawo karshen dauki-ba-dadin da aka shafe lokaci mai tsawo ana gwabzawa da ya yi sanadiyyar rayuka da dama. To amma duk da wannan sulhu da aka cimma na tsagaita bude wuta, har ya zuwa wannan lokaci rayuwar mata da kananan yara na cikin tsaka mai wuya har ma da magidanta da matasa da ke tunanin makomar rayuwarsu bayan yakin Tigray.
Karin Bayani: Yankin Tigray na fama da matsananciyar 'yunwa
Hukumomin rikon kwarya na yankin Tigray sun ce mutanen da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira daban-daban a lardin sun haura miliyan daya. Hukumomin sun ce dakarun Eritrea da ke taimakawa hukumomin Habasha suke kula da iyakokin yankin wanda hakan ke haifar da fargaba na komawar mutanen muhallansu. Jam'iyyar adawa ta Salsay Weyane Tigray ta zargi gwamnatin yankin da kuma ta tarayyar Habasha da jan kafa wajen mayar da mutanen muhallansu tare da sama musu makomar rayuwa mai inganci.
Hukumomin lardin Tigray sun bayyana cewa za a kashe sama da Dala biliyan $2.1 kwatankwacin Euro biliyan 2 domin sake tsugunar da ‘yan gudun hijrar, inda suke aiki da Majalisar Dinkin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki wajen neman tallafin taimakawa yankin daga kasashen ketare.