1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Ƙungiyar Tarayyar Turai dangane da Libiya

February 23, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da tattaunawar da take yi da Libiya akan wata yarjejeniya ta yaƙar baƙin haure da kuma sassauta manufofin ciniki tsakanin sassan biyu.

Catherine Ashton, kantoman ƙungiyar tarayyar Turai akan manufofin ƙetareHoto: AP

Ƙungiyar ta tarayyar Turai ba za ta ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Libiya a halin da ake ciki yanzu ba kamar yadda aka ji daga bakin kantoman ƙungiyar akan manufofin ƙetare Catherine Ashton. Tun a yammacin talatar da ta wuce ne Ashton ta tofa albarkacin bakinta dangane da halin da ake ciki a Libiya lokacin ziyarar da ta kai ƙasar Masar.

"Ina gabatar da kuka akan salwantar rayukan mutane, inda kuma Allah Waddai da matakan gallazawa tare da yin kira ga dukkan sassan da lamarin ya shafa da su nuna halin sanin ya kamata. Wajibi ne a girmama haƙƙin ɗan-Adam da walwala ga jama'a kuma ina fatan ganin mahukunta sun saurari koke-koken al'umar ƙasa."

Abin dake faruwa a Libiya kisan kiyashi ne

Jean Asselborn, ministan harkokin wajen ƙasar LuxemburgHoto: AP

A cikin wata hira da gidan rediyon Deutschlandfunk dake nan Jamus yayi da shi, ministan harkokin wajen ƙasar Luxemburg Jean Asselborn fitowa fili yayi yana mai cewar:

"A nawa ganin, abin dake faruwa a Libiya ba komai ba ne illa kisan kiyashi tsantsa. Abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne a yi bakin ƙoƙari wajen dakatar da wannan kashe-kashe na ba gaira a wani mataki na ƙasa da ƙasa."

Asselborn na tunani ne game da wani mataki na Majalisar Ɗinkin Duniya, alal-misali, domin bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Libiya da sauran sassa na duniya. Ta haka za a dakatar da malalar ƙarin sojojin haya zuwa ƙasar. Amma kuma Asselborn na sauraron ganin wani ƙwaƙƙwaran mataki daga ɓangaren ƙungiyar tarayyar Turai. A ganinsa wajibi ne ƙasashen ƙungiyar su ɗora hannu kan kadarorin shuagabannin Libiya dake ƙasashensu da kuma hana musu shiga ƙasashen. In har zarafi ya kama wajibi ne ƙasashen na Turai su rungumi duk wata asarar da wannan matakin zai haifar musu.

"Wijibi ne a ɗora duk wata maslaha ta tattalin arziƙin da za a iya samu daga wannan ƙasa, abin da ya haɗa har da man fetir da gas, akan mizani domin tantancewa ko shin ya kamata a ci gaba da ma'amalla da wannan ɗan kama-karya, inda ake hakala jama'a ba sani ba sabo."

An dakatar da cinikin makamai da Libiya


Dakatar da cinikin makamai da LibiyaHoto: Wikipedia/Nemo5576

Tuni dai hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai ta dakatar da dukkan tattaunawar da ake yi da Libiya game da yaƙi da baƙin haure da sassaucin manufofin ciniki. Kazalika dukkan ƙasashen ƙungiyar su 27 sun dakatar da cinikin makamai da Libiya. To sai dai kuma ƙasar Italiya na ɗariɗari da abin da zai biyo bayan matakan takunkumi kan Libiya. Domin kuwa ƙasar ba man fetir ne kaɗai take samu daga Libiyan ba, kazalika tana fargabar tuttuɗowar dubban-dubatar baƙin haure a cikinta. Kawo yanzun dai sauran ƙasashen ƙungiyar ba su nuna shirinsu na karɓar 'yan gudun hijirar dake ya da zango a Italiya da sauran ƙasashen dake gaɓar tekun baha-rum ba.

Mawallafi: Christoph Hasselbach/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal