1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin China da Rasha akan Siriya

Zainab MohammedJune 5, 2012

Vladimir Putin da Hu Jinatao sun sake jaddada matsayin gamayayyarsu na hawan kujerar naƙi tare da adawa dangane da matakan ƙasa da ƙasa akan Siriya.

epa03249669 Chinese President Hu Jintao (R) and Russian President Vladimir Putin (C) walk together after they reviewed an honor guard during a welcoming ceremony for the Shanghai Cooperation Organization (SCO) summit at the Great Hall of the People in Beijing, China, 05 June 2012. Russian President Vladimir Putin arrived in Beijing for talks that were expected to focus on Syria, bilateral energy cooperation, and other international issues. EPA/MARK RALSTON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A rangadinsa na kwanaki uku wanda ke zama na farkon irinsa a yankin Asiya tun bayan sake komawarsa karagar mulki a karo na uku, Putin ya nanata matsayin dangantakar ƙasashen biyu wa Hu jintao. A yayin wannan ziyara tasa dai ana saran Putin zai gana da shugabannin Iran da Afganistan, a gefen taron yankin, wanda ke zuwa makonni kalilan bayan soke ziyararsa zuwa Amurka. Ƙarin matsin lamba akan Syria wadda ke samun makamai daga Moscow dai, shine zai mamaye taron. Matsayin Beijing da Moscow akan rikicin na siriya dai, na ci gaba da yin karan tsaye wa ƙasashen larabawa dana tarayyar Turai, dangane da ɗaukar matakan ladabtarwa. A ranar litinin ne dai shugaban tarayyar turai Herman Van Rompuy ya shaida wa Putin a Rasha cewar, ya zamanto wajibi Duniya ta cimma matsayi kan rikicin na Siriya. Shima a farkon ziyararsa a yankin Gulf, ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Guido Westerwelle ya jaddada muhimmancin bin siyasa wajen gano bakin zaren warware rikicin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe