1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin EU ga boren adawa da gwamnatin Libiya

February 21, 2011

Ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatocin ƙasashen Larabawa

Catherine AshtonHoto: AP

Ministocin kula da harkokin wajen ƙungiyar tarayyar Turai sun gana a birnin Brussels na ƙasar Beljiam a wannan Lahadin, inda suka tattauna irin martanin daya kamata su mayar game da jerin zanga-zangar neman samar da sauye sauye ga tafarkin dimoƙraɗiyya a yankin arewacin Afirka da kuma Gabas Ta Tsakiya. Kantomar kula da manufofin ƙetare na ƙungiyar tarayyar Turai Catherin Ashton ta bayyana damuwar ta game da rigingimun da suka kai ga kissar masu zaga zanga a yankin tekun Fasha da kuma arewacin Afirka tun cikin watan Janairun.

A lokacin da take magana akan Libya kuwa, Mrs. Ashton, ta ce ƙungiyar tarayyar Turai ta buƙaci bin lamura sannu a hankali a ƙasar, kana da kawo ƙarshen tashe tashen hankula, tana mai ƙarawa da cewar tilas ne a zauna akan teburin shawara domin warware abinda ta ƙira halattattun buƙatun samar da sauye sauye.

A halin da ake ciki kuma, Libya ta yi barazanar katse bayar da duk wani haɗin kai ga tarayyar Turai wajen hana kwararowar 'yan gudun hijra, muddin dai ƙungiyar tarayyar Turai ta bayar da goyon bayan ta ga masu zanga zangar adawa da gwamnati. A lokacin da yake magana ta tashar telebijin da yammacin jiya,ɗan shugaban ƙasar ta Libya mai suna Saif Gadhafi ya ɗora alhakin ingiza zanga zangar akan masu son cimma burin kasuwancin su, da 'yan ƙetare da kuma waɗanda ya ƙira 'yan ta'adda.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammed Abubakar