Matsayin ICC game da ɗan Ghadafi
April 5, 2012Kotun duniya da ke hukunta manyan laifukan yaƙi ta nemi majalisar wucin gadin Lybiya ta miƙa mata ɗan tsohon shugaban ƙasa wato Saif al-islam domin fiskantar shari'a. Wannan mataki da kotun da ke hague ta ɗauka, ya biyo bayan watsi da ta yi da bukatar birnin Tripoli na jinkirta miƙa ɗan marigayi Ghaddafi. shi dai Sail al-Islama ya na daga cikin waɗanda kotun ta duniya ta ke zargi da kisan kiyashi lokacin da guguwar neman sauyi ta kaɗa a Lybiya a shekarar da ta gabata.
Ita dai majalisar wucin gadi ta so ne ta gudanar da shari'ar Saif al-islam a gaban wata kotu ta Libya. Hukuncin kisa za a yanke masa a cikin Libya idan aka same shi da laifin da ake zarginshi da aikatawa, yayin da a kotun duniya kuwa, za a yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal