1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban Ilmi da kuma matsalolinsa a tarayyar Nijeriya.

Abdullahi Tanko BalaNovember 25, 2009

A duk lokacin da aka yi maganar Ilmi a Nigeria tunani na farko da kan zo a zukatan jamaá shine faduwar darajar ilmin da lalacewar kayayyakin koyarwa da dai sauransu.

Yanayin ɗaukar darussa ga ɗalibai a Jamiá.Hoto: AP

Ilmi akan ce ginshikin cigaban alúma. Sai dai kuma wannan ɓangare na Ilmi musamman na Jamiá a tarayyar Nijeriya yana cin karo da matsaloli da dama waɗanda suka yi masa dabaibayi.

A duk lokacin da aka yi batun Ilmi a Nigeria tunani na farko da kan zo a zukatan jamaá shine faɗuwar darajar ilmin da lalacewar kayayyakin koyarwa da dai sauransu. Waɗannan matsaloli na buƙatar nazari da zurfin bincike domin faɗakar da waɗanda ke da ruwa da tsaki a harkar ilmin a game da yadda gazawarsu da rashin bada muhimmanci ga wannan ɓangare suka haifar da durƙushewa ko kuma taɓarɓarewar ilmi a ƙasar baki ɗaya.

A irin cigaban da da ake da shi yanzu a duniya, kusan kowane fanni na cigaban alúma ya taállaƙa ne akan Ilmi. To abin tambaya shine me yasa a Nigeria lamarin ya zama daban shin a ina matsalar take ? Yakubu Magaji Azare malami a jamiár Bayero ta Kano dake arewacin Nijeriya ya zayyana wasu daga cikin waɗannan matsaloli. " Rashin samun cikakken jarin da gwamnati take zubawa aɓangaren ilmi shine kashin bayan taɓarɓarewar ilmi a Nijeriya. Kafin a zo wannan matsayin taɓarɓarewa da ai anyi ilmin a Nijeriya kuma yayi muhimmanci yayi daraja. Aikin koyarwar kansa yayi daraja, yayi muhimmanci a idon alúma, domin a da idan kana malami a cikin alúmarku ana daraja ka ana ganinka da kima fiye da duk yadda kake tunani, amma mun wayi gari a kasarmu abinda kawai mutane suke gani da daraja shine kuɗi.

Waɗannan ɗalibai ne na kwalejin kimiyya da fasaha dake Kigali a ƙasar Rwanda.Hoto: picture-alliance / dpa

Ƙwararrun masana harkar ilmi sun yi nuni da buƙatar baiwa ɓangaren ilmin muhimmancin da ya wajaba domin ciyar da ƙasa da alúmarta gaba. Domin ganin tabbatuwar cigaban jamiói dama ilmin baki ɗaya, a wasu lokutan malaman jamioi kan shiga takun saƙa da gwamnati wadda suke ganin tana yiwa ilmin shakulatin ɓangaro. Malam Yakubu Azare yace babban abin takaici na irin halin da Jamioi ke ciki a Nijeriya, babu isasun kuɗaɗe da kuma gine ginen wuraren da yara zasu yi karatu. Yace alal misali a duk shekara yara sama da miliyan ɗaya suke zaunawa zarrabawar shiga jamioi da hukumar JAMB take shiryawa. To amma dukkan jamioin basu da gurbin ɗaukar abinda ya haura yara 220,000 a cikin miliyan ɗaya. A wasu jamioin za ka tarar malami ɗaya ya tsaya a gaban ɗalibai fiye da 500 yana koyar da su. Dukkaninsu a takure, babu wuta, yara na gumi malami na gumi.

A yanzu dai makarantu masu zaman kansu na ƙara yawaita a ƙasar Nijeriya ciki kuwa har da Jamioi. A cewar Malam Yakubu Azare sau da dama jamaá kan ringimo abubuwan da ko dai basu kai matsayin yinsu ba ko kuma idan ma sun kai, to akan samu matsala a tsarin da suke aiwatar dasu domin kuwa ya kan zo a gurgunce. Ana buɗe waɗannan makarantu ne don neman kuɗi ba wai saboda ruhin cigaban ilmi ba. Amma saboda matsuwa da ɓukatar yin karatun yake jawo yara suke shiga waɗannan makarantu. Kuma ɗaya daga cikin abin da hakan zai haifar shine kullum zaá cigaba da samun rashin ƙwarewa na waɗanda suke yin karatun da kuma ƙara taɓarɓarewar ilmi.

Ɗaliban makaranta a Togo.Hoto: dpa

A nata ɓangaren gwamnatin ta sha nanata cewa Dambu idan yayi yawa baya jin mai, bisa laákari da irin nauyin da ya rataya a wuyanta inda kowane ɓangare kama daga ilmin da harkar lafiya da ayyukan noma da samar da abubuwan buƙatun rayuwa ga alúma duka suka dogara akan gwamnati. A saboda haka tace tana bakin ƙoƙari, hasali ma dai tace an sami cigaba a ɓangaren ilmin idan aka kwatanta da shekarun baya.

Sai dai a cewar Malam Tukur Abdulƙadir na Jamiár jihar Kaduna yace batun cewa an sami cigaba ga harkar ilmi a Nigeria yaudarar kai ne kawai yace idan ka shiga makarantu musamman a arewacin Nijeriya babu abinda zaka gani sai ɓacin rai.

Rashin bada ƙwarin gwiwa da ƙarfafawa ga malamai ya sanya ƙasar na hasarar ƙwararun malamai waɗanda ke yin ƙaura zuwa ƙasashen Turai da Amurka ko kuma manyan kamfanoni inda zasu fi samun albashi mai tsoka. Dama shi malamin makaranta abin da yake buƙata shine a kyautata masa albashinsa a bashi kayan aiki ya zamana kuma yana da inda zai kwanta a rayuwarsa.

Cunkoson ɗalibai da yanayin koyo da koyarwa a Jamiá.Hoto: picture-alliance / su5/ZUMA Press

Malaman makarantu a Nijeriya na ganin cewa baá makara ba idan har ana so a ceto ilmin daga durƙushewa. Yakubu magaji Azare na jamiár Bayero ta kano yace abu ne mai sauƙi idan gwamnati na so ta yiwa ilmin gata. Yace Nijeriya Allah yayi mata arziki mai yawa. Idan gwamnati zata ware wani kaso daga cikin abinda ake samu na rarar man Fetur kamar yadda aka yiwa hukumar PTF a wani lokaci can a baya, zai taimaka wajen bunƙasa ilmi ta hanyar samar da kayayyakin koyarwa a dukkanin makarantu da Jamioi da samar da gine-gine na ɗakunan karatu da kuma kyautata jin daɗin malamai. Idan an yi haka kasa zata cigaba domin cigaba baya samuwa sai da ilmi.