1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Jamus game da rikicin Masar

November 21, 2011

Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya bayyana juyayi game da halin rikici da Masar ta shiga

Guido Westerwelle tare da Mohammed Tantawi a birnin Alkahira.Hoto: picture alliance/dpa

Gwamnatin tarayya Jamus ta bayyana matukar juyayi game da saban rikicin da ya barke a kasar Masar.

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce yawan mutanen da suka rasa rayuka da kuma wanda suka ji raunuka na tayar da hankali.

Rahotani daga dandalin Tahrir inda masu zanga-zangar suka ja daga,sun ce fiye da mutane 30 suka rasa rayuka, sannan fiye da dari biyu suka ji raunuka a cikin arangama da jami´an tsaro.Guido Westerwelle ya yi kira ga gwamnatin rikwan kwarya Masar, ta dakatar da wannan kisan gilla ga jama'a.

Shima ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague, ya bayana fatan kasarsa game da Masar:

"Muna bukatar ganin Masar ta tabbata bisa takarfin demokradiya, muna bukatar samar da kundin tsarin mulki kyakkyawa wanda ya kunshi cikkaken tsarin mulki da kuma kare hakkokin jama'a"

Wannan rikici shine mafi muni tun bayan kifar da Hosni Mubarak daga karagar mulki a farkon shekara da muke ciki.Sabin tashe-tashen hankula na wakana a yayin da ya rage 'yan kwanaki kalilan kamin zaben 'yan majalisa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal