Matsayin Japan akan makamashin nukiliya
August 7, 2012Ministan kula da harkokin masana'antu a kasar Japan ya tofa albarkacin bakinsa game da muhawar da ake ci gaba da tafkawa a kasar akan manufar da ta shafi makamashin nukiliya, inda ya ce kasar na iya yin watsi da shirin nukiliyar ta nan da shekara ta 2030, ba tare hakan yayi mummunan tasiri ga tattalin arzikin ta ba, wanda ke zama na ukku mafi girma a duniya. Yukio Adano ya shaidawa manema labarai cewar mai yiwuwa ma yin watsi da cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliyar ya taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin, ta hanyar yin hubbasa wajen inganta makamashin da ake sabuntawa, wanda kuma ka iya biyan bukatun cikin gida.
Furushin ministan masana'antun dai ya zo ne a dai dai lokacin da hukumomin Japan ke ta yin kokarin bullo da sabuwar manufar bunkasa makamashin da ake sabuntawa bayan hatsarin Fukushima a shekarar da ta gabata, wanda ya tilastawa kasar rufe wasu cibiyoyin samar da wutar lantarkin ta har guda 50.
Sai dai kuma tuni firaministan kasar Yoshihiko Amano ya bayar da umarnin farfado da aikin biyu daga cikin cibiyoyin yayin da kasar ke fuskantar matsalar karancin wutar lantarki, lamarin daya janyo boren adawa daga bangaren masu yin suka ga yin aiki da makamashin nukiliya a kasar ta Japan.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu