1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin MDD kan harin Isra'ila

June 1, 2010

Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya yayi Allah wadai da hallaka jami'an agaji da sojojin ƙundunbalar Isra'ila suka yi

Zaman taron kwamitin sulhuHoto: picture-alliance/ dpa

Kwamitin sulhu na majalisar Ɗinkin duniya yayi Allah wadai da matakin da Isra'ila ta ɗauka na kai hari kan jiragen ruwa da ke ɗauke da masu fafutikar kai kayan agaji i zuwa zirin gaza. A lokacin wani zaman gaggawa da yayi, kwamitin ya yi kira da a gudanar da binciken ƙasa da ƙasa domin gano gaskiyar abin da ya faru. Aƙalla mutane tara ne dai sojojin ƙudun balar Isra'ila suka hallaka, a lokacin da suka yi dirar miƙewa akan ɗaya daga cikin jiragen ruwan ƙasa da ƙasa a tekun Gaza.

Wasu daga cikin ƙasashe da ke da kujerun dindindin a kwamitin majalisar da suka haɗa da Faransa, da Rasha da kuma Sin sun nemi Isra'ila da ta ɗake shingen da ke taƙaita zirga-zirga i zuwa zirin gaza. ƙasar Amirka a nata ɓangaren ta nemin Isra'ila da ta sassauta takunkumin da ta ƙaƙaba ma zirin na Gaza. ƙasar Turkiya ta bukaci a gudanar da taron gaggawa na ƙungiyar tsaro ta Nato bayan da ta danganta wannan hari na Isra'ila da ta'addanci.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu