Matsayin tsarin mulkin Najeriya dangane da barin jam'iyyar siyasa
January 21, 2014Talla
Tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ko dai 'yan majalisar dokoki ko kuma gwamnoni damar ficewa daga jam'iyyar da aka zabesu a karkashinta, muddin dai jam'iyyar tana fuskantar rigingimu ko kuma ta rushe.
Masana harkokin shari'a sun nunar da cewar inda za a fuskanci matsala shi ne idan jam'iyya na dunkule, babu rarrabuwar kawuna a cikinta.
Domin karin bayani, za ku iya sauraren shirin a kasa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane