Najeriya: Auren wuri ga yara kanana
January 22, 2025Matsatsin rayuwa na tilatsa iyaye daukar matakai na samun sauki da kuma yadda za su kula da iyalansu domin samun mafita.
Daga cikin matakan da iyaye ke dauka a wannan lokaci shi ne na cire ‘ya ‘yansu mata daga makaranta tare da yi musu aure saboda ko ba komai sun samu saukin kashe kudi domin karatunsu da ma dawainiyar ciyarwa da tufatar da su.
Wannan yasa aka samu karuwar ‘ya‘yan da ake cire su daga makaranta ana yi musu aure da ma karuwar ‘yan mata da ke yawon talla ba tare da zuwa makaranta ba lamarin da yake kara jefa rayuwarsu cikin hadari da kuma haifar da koma baya a kokarin karfafa ilimin ‘ya‘ya mata a yankin.
Malama Safiya Muhammad wata uwa ce a Maiduguri ta baiyana dalilin da ya sa iyayen ke fitar da ‘ya‘yan su mata daga makaranta a wannan lokaci.
"Da wanne za mu ji kudin makaranta ko kudin motar zuwa makaranta. Ko abincin da za a ci a gida?. Iyaye ya zama musu dole su cire ‘ya‘yansu daga makaranta su yi musu aure. kowa ya san halin da ake ciki a kasar nan na matsatsin rayuwa”
Masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi da masu kare hakkin ‘ya‘ya mata sun bayyana damuwa kan wannan hali da ake ciki wanda suka ce ba sune mafita ga halin da iyayen suke ciki ba inda kuma suka bukaci gwamnati ta gaggauta daukar matakai na magance wadannan matsaloli domin a karfafa ilimi ‘ya‘ya mata. Malama A'isha Abubakar wata mai gwagwarmayar kare hakkin mata ce a Najeriya.
"Abu ne wanda ni da kai ba zamu iya magance shi ba. Abu ne wanda yake bukatar hannu da yawa, Gwamnati da al'umma da kungiyoyi masu zaman kansu har da mu iyaye. A samo sana'a wanda yarinya za ta iya yi a zaune a gaban iyayenta kaga an sa ta zama mai dogaro da kanta za ta iya kula da kanta za ta iya rufa wa kanta asiri.”
To sai dai gwamnatoci a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da suka ce suna sane da halin da ake ciki sun ce suna daukar matakai na magance hakan ta hanyar bayar da kudin tallafi ga ‘yan matan. Malam Abubakar Baba shine Baturen Ilimi na karamar hukumar Gombe.
"Gwamnatin jihar Gombe ta dauki matakin gaggawa inda ta hada kai da hukumar bada agaji ta AGILE suna tura wa iyayen yara kudi Naira dubu ashirin (N20,000) kowane zangon karatu. Sannan kuma idan suka gama karatu a zango na daya da na biyu da na uku zuwa canjin aji za a tura wa iyayen yaran Naira budu Talatin (N30,000) don su dauki nauyin ‘ya‘yan su da suke zuwa makaranta musamman mata”
Kasa magance wannan matsala a wannan shiyya ta arewa maso gabashin Najeriya dai ka iya zama nasara ga kungiyar Boko Haram wacce ke yaki da karatun Boko musamman ga ‘ya‘ya mata.