Matukan jiragen saman Lufthansa na ci gaba da yajin aiki
March 19, 2015Talla
A wannan Alhamis dubun dubatan matafiya tsakanin kasa da kasa sun shiga halin rashin sanin tabbas, sun kuma tagaiyara sakamakon yajin aikin matukan jiragen saman kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Lufthansa na nan Jamus, wanda kuma suka fadada shi zuwa bangaren jiragen sama masu zirga-zirga ta dogon zango. Fasinjoji dubu 18 yajin aikin na wannan Alhamis ya shafa bayan an soke tashin jirage masu cin dogon zango 84 daga cikin 153. Kamfanin Lufthansa ya ce a dole zai soke tashi da saukan jirage 790 a ranar Jumma'a, lamarin da zai ta'azzara mawuyacin halin da fasinjojinsa ke ciki. Matukan jiragen saman na Lufthansa na yajin aikin ne saboda rashin cimma daidaito game da wani tsarin fansho.