1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawuyacin hali ga mazauna yankin Nuba

August 9, 2012

Yankin tsaunukan Nuba dake kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu ya zama wani filin daga, abin da ya jefa mazauna yankin cikin halin lahaula.

Hungern oder Fliehen - Zur Situation in den Nuba-Bergen im Sudan Kinder, die wegen der ständigen Gefahr von Luftangriffen nun in diesen Höhlen leben. Wie überhaupt die Bevölkerung. Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Bettina Rühl Wann wurde das Bild gemacht?: 18.05.2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Tongole, Nuba Berge ***Bild darf ausschließlich für den Artikel "Hungern oder Fliehen - Zur Situation in den Nuba-Bergen im Sudan" genutzt werden***
Hoto: Bettina Rühl

An bawa Sudan ta Arewa mallakin yankin duk da cewa al'ummarsa sun fi ɗaukar kansu a matsayin 'yan Sudan ta Kudu. Sojojin saman Khartoum na yawaita kai farmaki a kan wuraren fararen hula a yankin na Nuba, dake ƙarƙashin ikon jam'iyar adawa ta 'yanto al'umar Sudan wato SPLM. A halin da ake ciki da yawa daga cikin ƙungiyoyin agaji sun fice daga yankin, abin da ya ƙara jefa mazauna cikin wani mummunan bala'i. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ke zaman tattauna batun Sudan ɗin a wannan Alhamis.

Mawaƙan wata majami'ar Katholika kenan a garin Gidel dake a yankin tsaunukan Nuba suna rera baitocin Allah Ya ba su zaman lafiya. A wannan karon hankalinsu na kan baitin maimako a sama, domin a kullum jiragen saman yaƙi na yawaita shawagi a sararin samaniyar yankin.

Tsere wa hare haren jiragen sama

Tun a farkon watan Yunin shekarar 2011 yankin na tsaunukan Nuba ya faɗa cikin yaƙi, inda shugaban Sudan Omar al-Bashir ya ƙyale jiragen saman yaƙi na kai hare hare a kan al'ummarsa. Barabas Kuku shi ne wakilin gwamnatin 'yan tawayen garin na Gidel.

Mafaka a cikin ƙogoHoto: Bettina Rühl

"Ina ƙoƙarin magance wasu matsaloli da mutane ke fuskanta. Da yawa na tserewa zuwa Yida dake dab da kan iyaka da Sudan ta Kudu, wasunsu na ƙarasawa zuwa Kudanci ko Kenya ko kuma wasu wurare dabam."

Rayuwa a tsunukan Nuba kusan ba ta yiwuwa, domin da gangan sojojin sama suke kai farmaki kan mutane waɗanda ke jiran ɗebo ruwa daga rijiyoyi ko a kan makiyaya da manoma a gonaki. Hakan ya sa mutane ne tsoron zuwa gonakinsu. Daga cikin waɗanda wannan ta'asa ke rutsa wa da su har da mata da ƙananan yara. Al'ummar yankin na fama da matsananciyar yunwa, sannan ba a iya gudanar da wani aikin agaji na ƙasa da ƙasa, domin shugaba al-Bashir ya toshe hanya ɗaya tilo dake shiga yankin tsaunukan daga Sudan ta Arewa. Haka na kawo ciƙas ga aikin jin ƙai. A ma halin da ake ciki kusan dukkan ƙungiyoyin agaji sun ƙaurace wa hare haren ta sama. In banda ɗaiɗaikun fastoci da majami'ar El Obeid wadda ke kula da asibitin garin Gidel. Malda wata 'yar shekaru 22 a duniya na jinya a asibitin na mummunan ƙuna da ta samu a fuska, hannu da ƙafafu.

Yaƙin ya fi shafan fararen hula

"Wani bam ya rutsa da ni. Ina cikin bukka lokacin da jirgin saman ya kai hari. Da ni da 'ya'ya na mun yi ƙoƙarin ɓuya amma mun makara. Mu biyar ne da ni da 'ya'ya na biyu da kuma wasu mata biyu. 'Ya'ya na da wata mata sun mutu nan take."

Matsalar yunwa ta sa dole an koma ga cin ganyeHoto: Bettina Rühl

Tom Catena likita ne Ba-amirke dake kula da marasa a asibitin ya ce a lokacin nan ya samu majinyata da yawa dake da irin wannan mummunan ƙunan harin bam wanda ya ce ba bam ne da aka saba ganin irinsa ba.

"Idan ba samfurin Napalm ba ne to wani abu ne makamancinsa, wataƙila an haɗa da fetir wanda da zarar ya fashe sai gobara ta tashi. Wannan shi ne kaɗai abin da zan iya cewa domin ƙunan ya yi muni."

Dukkan majinyata akasari yara a asibitin, rauni iri ɗaya suke samu wato ƙuna a hannu, ƙafafu, fuska da kuma baya. Wannan yaƙi dake zaman wani ta'addanci a kan al'umma ya fi shafan fararen hula.

Mawallafa: Bettina Rühl / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi