May na neman goyon baya kan wa'adin Brexit
April 9, 2019Firaministar Birtaniya Theresa May na wata ziyara a wannan Talata a kasashen Jamus da Faransa inda za ta gana da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma Shugaba Emmanuel Macron da zimmar kamun kafarsu, ga bukatar sake tsawaita mata wa'adin ficewar Birtaniya daga EU zuwa 30 ga watan Yuni a maimakon 12 ga wannan wata na Aprilu.
A gobe Laraba ne dai May za ta gabatar wa kasashen na Turai da wannan bukata tata a taron koli na birnin Brussels. Sai dai tun kafin zuwan na May a biranen Berlin da Paris, kakakin Merkel Steffen Seibert, ya ce tattaunawar kafin zuwa taron na birnin Brussels na da muhimmanci ta la'akari da sarkakkiyar da ke tattare da batun.
Amma daga nashi bangare Shugaba Macron ya bayyana cewa bukatar tsawaita wa'adin ta zo da wuri, a kan haka ne ya bukaci Birtaniyar da ta gabatar masa da kwararran hujjoji na fa'idar tsawaita wa'adin ficewar Birtaniyar daga cikin kungiyar ta EU.