1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

May ne neman bunkasa kasuwanci da Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
August 28, 2018

Firaministar Birtaniya Theresa May na ziyara a kasashen Afirka uku inda ta fara da Afirka ta Kudu da nufin samun madogara a fannin tattalin arziki bayan ficewa daga Kungiyar Tarayyar Afirka.

Theresa May in Südafrika
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Firaministar Birtaniya Theresa May ta aza harsashin sabuwar dangantakar kasarta da takwarorinta na Afirka da nufin magance gibin tattalin arziki da za ta iya fuskanta idan ta raba gari kwata-kwata da kungiyar Tarayyar Turai. Cikin jawabin da ta yi bayan isarta birnin Cap na Afirka ta Kudu, May ta sanar da burinta na sanya Birtaniya a sahun farko na kasa mai karfin arziki da ke huldar kasawanci da Afirka kan nan da shekara ta 2022.

Tun bayan kuri'ar raba gardama na ficewa daga EU na watan Maris na 2016, London ta matsa kaimi a fannin diflomasiyya don samun karin yarjejeniyoyin kasuwanci da za su maye gurbin wadanda take da su da kungiyar Tarayyar Turai. Theresa may ta  bayyana matakin zuba jari na dala miliyan dubu hudu a kasashen Afirka . Birtaniya ta kasance a matsayi na biyu na kasashen da suka fi zuba jari a Afirka baya ga Amirka.

Baya ga Afirka ta Kudu, Firaministar Birtaniya za ta je Najeriya don ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, kafin ta wuce Kenya ranar Alhamis.