MayaƘan taliban sun kashe sojan Britania ɗaya.
August 27, 2006Talla
Mayakan Taliban sun sake kashe soja ɗaya ɗan ƙasar Britania, a wani saban hari da su ka kai yau, a kudancin ƙasar Afghanistan.
Kakakin ministan tsaro a birnin London ,ya ce harin ya wakana, a yammacin jihar Helmand.
Tun ƙarshen watan juli da ya gabata, rundunar tsaro ta NATO, ta karɓi jagorancin sojojin ƙawance a Afgahinstan, a yaƙin da su ke, na kakkaɓe yan taliban.
Daga wannan lokaci, ya zuwa yanzu, ƙungiyar NATO, ta yi assara sojoji 6.
A halin yanzu,Ƙasar Afghanistan, na fuskantar tashe tashen hankulla mafi muni, tun bayan kiffar da yan taliban a shekara ta 2001.