Mayaka daga waje na son hana Siriya sakat
May 21, 2025
Tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Assad, shugabannin kasashen yammacin duniya sun gargadi sabuwar gwamnatin Ahmad al-Sharaa game da bai wa masu tsattsauran ra'ayi daga kasashen waje mafaka. Tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2013, kungiyar 'yan tawayen Hay'at Tahrir al-Sham ta narke cikin kungiyar IS, kafin ta koma kawance da al-Qaeda. Bayan yanke hulda da al-Qaeda a shekarar 2016, Hay'at Tahrir al-Sham ta shafe kusan shekaru 10 tana yakar IS a sassan kasar da take iko da su. Tasirin kungiyoyin ta'adda a Sirfiya, ya shafa mata kashin kaji na zama saniyar ware da sauran manyan kasashen duniya. Matakin da Farfesa Eyal Zisser na jami'ar Tel Aviv ke cewa shi ne tushen wargaza tubalin Siriya.
Karin Bayani:Shugaban Siriya na ganawa da shugabannin kasashe
"To, wadannan takunkumi ne masu kaifi wanda a zahiri ya kai ga rugujewar gwamnatin Assad har ma ita kanta sabuwar gwamnatin yanzu, idan da ba a fara dage mata takunkuman ba."
Sai dai a gefe guda, ana ganin faduwar gwamnatin Assad, tamkar ikirarin kashe maciji ne ba a sare kansa ba. Bayan da IS ke kira ga mayakan kasashen waje da su yi wa sabuwar gwamnatin tawaye musamman wadanda ke adawa da dasawar diflomasiyya tsakanin kasar da Amurka. Trump, ya murza kambunsa lallai al-Sharaa ya fatattaki 'yan ta'addan kasashen waje daga Siriya, don samun sassaucin takunkumi, sharudan da kasashen Faransa da Jamus suka ba wa Siriya don gudun kitso da kwarkwata. Kaja Kallas, ita ce babbar jami'ar diflomasiyyar kungiyar tarayyar Turai.
Karin Bayani:Doland Trump ya dage takunkumin da Amurka ta sanya wa Siriya
"Ba za a iya samun zaman lafiya ba tare da habaka tattali arziki ba, kuma dukkanmu muna bukatar tsayayyiyar Siriya. Muna bukatar mu ba wa al'ummar kasar Siriya dama."
A halin da ake ciki, da wuya a san ainihin adadin baki masu yaki tare kungiyar HTS. Ana hasashen tsakanin 1,500 zuwa 6,000, mafiya akasari 'yan Uygur, wadanda yawancin yan Siriya ke kira "Turkistan," daga tsakiya da Gabashin Asiya, da kuma kasar China.
Sauran mayakan sun fito daga Rasha da wasu tsoffin jihohin Soviet da Balkans da Turkiyya da kuma kasashen Larabawa daban-daban. Yawancinsu sun shigo Siriya ne a lokacin yakin basasar kasar domin amsa kiraye-kirayen kungiyar IS da ke kokarin kafa daula a wancan lokaci.
A karshen shekarar 2024, a lokacin da kungiyar HTS ta jagoranci hambarar da gwamnatin Bashar al Assad na Syria, yawancin mayaka daga wajen Siriya da suka hada da 'yan kabilar Uygur da Checheniya, sun taka muhimmiyar rawa a nasarar yakin.
Shugaban gwamnatin na Siriya Al-Sharaa ya ce ya kamata a basu tukwicin kokarinsu, wannan ya sa a watan Janairu, an nada wasu mayaka daga kasashen waje a manyan mukamai a cikin sabuwar rundunar sojojin kasar, matakin da ya haifar da cece-kuce.
Karin Bayani:Siriya ta fara dawowa cikin dangi
Ina makomar mayakan kasashen waje a sabuwar gwamnatin Siriya? Wannan ita ce babbar ayar tambaya, yayin da kasar ke na'am ga bukatun kasashen yammacin duniya don samun sassaucin takunkumin da kasar ke ciki. Bayan ganawar al-Sharaa da Trump, an yi zargin jami'an tsaron Syria sun kai farmaki kan sansanonin mayakan kasashen waje a Idlib, sai dai wasu na cewa akwai kila wa kala.