An kashe sojojin Burkina Faso
January 29, 2020Talla
Mayakan sun sa bam a jikin motar sojojin tare da bude musu wuta yayin da suke sintiri daga garin Madjoari zuwa Pama da ke gabashin lardin Kompienga na kasar ta Burkina Faso.
Wannan sabon harin ya faru bayan wani mummunan hari da ya halaka fararen hula akalla 50. Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai sun kashe mutane akalla 800 tare da tilasta kusan 6,000 gudun hijira a Burkina Faso tun bayan tsanantar matsalar rashin tsaro a 2015, abin da ake ganin ya fara shafar makotan kasashe kamar irin su Mali.