1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayaka sun kwace kauye a tsakiyar Mali

Abdul-raheem Hassan
January 30, 2020

Mazauna kauyen Soloko sun ce 'yan bindigan sun dasa tutarsu a sansanin sojojin, bayan wani harin da ya kashe sojoji 20 kwanakin baya-bayannan.

Mali Unruhen l Erneuter Angriff auf Soldaten - Symbolbild
Hoto: Imago/Le Pictorium/N. Remene

Rayuwar mutanen da ke kauyen Soloko na cikin hatsari tun bayan da mayakan suka ayyana kwace iko da garin, mazauna garin sun koka da jinkirin samun agaji daga jami'an tsaro. Kauyen Soloko shi ne kauye na karshe a kan iyakar Mali da kasar Mauritaniya, kauyen na kusa da wani ungurminn daji da ke zama sansanin duk 'yan ta'adda da ke alaka da kungiyar al-Ka'ida wadan da ke kai hare-hare a kasashen Sahel musamman Burkina Faso da Nijar da Mali.