Mayakan Al-Shabaab sun kai hari a Mogadishu
June 25, 2016Talla
Da farko dai maharan sun soma da jefa wasu ababe masu tarwatsewa, kafin daga bisani su buda wuta da bindigogi masu sarrafa kansu. Wani mutum mai suna Abdihafid Mudey, da ke kusa da otel din da ake kira Naasa Hablood, ya tabbatar cewa har ya zuwa wajejen karfe biyar na yamma ana ta harbe-harbe cikin otel din. Sai dai ba su san abun da ke faruwa ba, domin a daidai lokacin da yake sanar da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP wannan labari, yana kwance ne a kasa domin tsira da rayuwarsa.
Wasu majiyoyi da dama na ma'aikatar tsaron kasar sun tabbatar da wannan hari, wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla biyar cikinsu jami'an tsaro uku, tare da jikkata wasu mutane shida.