Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi
November 11, 2024Ma'aikatar tsaron kasar Chadi ta sanar da cewa sojojin Chadi 15 ne suka mutu a yayin da wasu fiye da suka jikkata ke samun kulawar gaggawa a wani asibitin birnin N'Djamena, biyo bayan wata aranagamar da dakarun kasar suka yi da mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.
Karin Bayani : Sojojin Chadi sun kashe 'yan Boko Haram da dama
Ma'aikatar tsaron kasar ta ce sojojinta sun yi nasarar kashe daruruwan mayakan Boko Haram da ta kaiwa takakka a tunga da mabuyar mayakan kungiyar a sansanonisu na Tafkin Chadi.
Karin Bayani : Kulla alakar tsaro tsakanin Chadi da Nijar
A karshen watan Oktoba gwamnatin kasar Chadi ta kaddamar da shirinta na Operation "Haskanite" wato Karagiya, da ke da nufin kakkabe mayakan Boko Haram da suka kai wa wani sansanin sojanta hari tare kisan fiye da soji 40.