1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila na son kutsawa cikin ramukan Hamas

October 23, 2023

Ramukan karkashin kasa da kungiyar Hamas ta gina kuma take samun mafaka a cikinsu a Zirin Gaza, na ci gaba da haifar da tarnaki ga Isra'ila wacce ke hankoron kutsawa ciki.

Commemoration of the 2014 war, the 51-day period of the Israeli-Palestinian conflict in Gaza, Palestine - 20 Jul 2023
Hoto: picture alliance / ZUMAPRESS.com

Manyan-manyan ramuka na karkashin kasan na kungiyar Hamas dai sun kai kusan 1,300 da ke warwatse a kusurwa dabam-dabam ta Zirin Gaza. Rahotanni sun ce kun kowane rami ya kai tsawon kimanin kafa 230 a karkashin kasa, an kuma ginasu da fadin da dan Adam zai yi rayuwa a ciki ba tare da wata matsala ba. Dalilin ke nan da masana irinsu Mike Martin na kwalejin horas da dabarun yaki ta  Kings College da ke London ganin hakan a matsayin babbar barazana ga Isra'ila wacce ke da muradin kutsawa Zirin Gaza da dakarunta ta kasa.

Babban kalubale a gaban sojojin Isra'ila wajen shiga ramunka Hamas

Hoto: JINI/Xinhua/picture alliance

Kalubalen gaza tantance wane ne soja, wane ne kuma farar hula a Zirin na Gaza, na kawo komabaya a wannan rikici. A saboda haka fada gaba-da-gaba abu ne mai wahala ga Isra'ila, domin za su fuskanci harbe-harbe daga kasa da sama da ma wurin da ba su yi tsammani ba. Idan kuma sun rusa gidaje, nan ma mayakan Hamas za su iya samun wajen buya a cikin baraguzan kasa. Gaskiyar maganar ita ce yaki gaba-da-gaba ta kasa abu ne mai matukar wahala ga kowane soja. Masana na cewa akwai alamun mutanen Isra'ila kusan 200ko sama da haka da Hamas ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba ana tsare ne da su a cikin wadannan ramuka. A cikinsu, kungiyar Hamas da kasashen Amirka da Jamus da Tarayya Turai suka bayyana ta matsayin ta ta'addanci ke ajiyar abinci da ruwan sha da janareta da sauran kayan aikin da take bukata wajen kai hare-hare ga Isra'ila. Bincike ma ya tabbatar da cewa manyan jagororin Hamas na samun mafaka ne a cikin irin wadannan ramuka na boye. Masanin yaki Mike Martin na cewa lamarin ya zamar wa Isra'ila abu mai sarkakiya. 

Ramuka sun fi sama da guda dubu kuma kowane na da girman da dan Adam zai rayu a ciki

Hoto: Alexi J. Rosenfeld/Getty Images

Gaskiya ne, akwai dabaru dabam-dabam da za a iya gano irin wadannan ramuka ta hanyar na'urori da bayanan sirri, amma ni fargabata guda daya ce. Akwai rauni a bangaren tattara bayanan sirri na sojojnin Isra'ila tun da har suka gaza gano cewa za a kai musu babban hari irin wanda aka kai musu. Kuma ina ganin kuskuren na a wajen ma'aikatan da ke yi musu wannan aiki ba wai daga na'ura ba.''Tun a shekara ta 2014,gwamnatin Isra'ila ta gano cewa kungiyar Hamas na gina maboya a karkashin kasa. Hukumomin Isra'ilan sun yi hobbasa na ganin sun dakile Hamas gina wadannan ramuka. Amma kuma matsalar ita ce babu wanda yake da tabbacin hatta a cikin gidansa da ke cikin Isra'ila babu ramin na Hamas a karkashinsa. To ina mafita ke nan? Za a iya amfani da na'ura a tattaro bayanan sirri kan maboyar makamai da ma wuraren da dakarun Hamas masu amfani da na'urori a jikinsu suke. Amma abu ne mai wahala, na'urar ta samar da kammalallen bayanan sirrin da ake bukata domin tunkarar mayakan, kuma ina ganin Isra'ila na da gibi sosai a wannan fannin. A takaice akwai alamomin tambaya a kan abin da karfin sojijn Isra'ila zai iya da kuma ba zai iya yi ba. Zabin da ke gaban Isra'ila a wannan yakin da take da Hamas dai a cewar masana, shi ne ci gaba da kai farmaki ta sama na tsawon lokaci wanda ka iya ba ta damar sanin takamaiman wuraren da wadannan ramuka da tsayinsu ya kai kimanin kilomita 500 suke.