'Yan Houthi sun hallaka wani kwamandan Saudiyya
December 14, 2015Talla
Kanar Abdullah Al -Sahyan wanda ke jagorantar rundunar Saudiyya a Yemen ya mutu ne sakamkon wani makami da 'yan tawayen Houthi suka harba kan sansanin sojojin da ke a Lardin Taiz na yeman ata cewar wata majiya da ke futowa daga kasar.
Ana dai sa ran a ranar talatar nan ce 'yan tawayen Houthi da jami'an gwamnatin Yeman za su yi wani zaman tattaunawa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Switzerland domin kawo karshen yamutsin watanni tara da kasar take fama da shi.