Mayakan IS sun fice daga birnin Ramadi na Iraki
December 27, 2015Talla
Mayakan kungiyar IS mai neman kafa daular Islama sun janye daga tungarsu ta karshe da ke birnin Ramadi na kasar Iraki, abin da ke zama nasara mafi girma ga sojojin gwamnati. Dakarun da ke yaki da ta'addanci sun shafi kwanakin da suka gabata suna kazamin fafatawa a wani ginin gwamnati.
Majiyoyin asibiti sun ce jami'an tsaro kusan 100 suka samu raunika lokacin wannan fafatawa. Dakarun gwamnatin na Iraki sun samun tallafin mayaka Musulmai mabiya tafarkin Sunni gami da rakiyar jiragen saman yakin kasashen kawancen da Amirka ke jagoranta. Dakarun na kawance sun kuma kai farmaki biranen Mosul da Fallujah wadanda suka rage a hannun mayakan na IS.