Mayakan IS sun halaka limami a Siriya
January 8, 2015![IS Kämpfer Archivbild 2013](https://static.dw.com/image/18039999_800.webp)
Talla
Da yammacin ranar Alhamis ne mayakan na IS suka sare kan wani limamin masallaci a garin Abu Khuyut a kusa da birnin Hasakeh a Arewa maso gabashin Siriya a cewar Kungiyar kare hakkin bil'Adama da ke sanya idanu kan rikicin kasar ta Siriya.
A cewar kungiyar mai sanya idanu da ke da sansani a Birtaniya uku daga cikin 'ya'yan malamin na daga cikin mayakan na kungiyar IS. Wannan kuma na zama karon farko da masu ikirarin jihadin sukan halaka wani malamin addini .