1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mayakan ISWAP sun halaka kwamandan sojin Najeriya

November 17, 2025

Tun da farko kafun ISWAP ta fitar da labarin, rundunar sojin kasar ta musanta kashe kwamanda M. Uba.

Rundunar sojin Najeriya ta fada cewa sojoji hudu sun rasa rayukansu yayin harin kwanton baunan
Rundunar sojin Najeriya ta fada cewa sojoji hudu sun rasa rayukansu yayin harin kwanton baunanHoto: AFP/Getty Images

Mayakan Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun ce sun kashe wani babban jami’in sojin Najeriya da suka kama a wani mummunan harin kwanton bauna da suka kai wa ayarin soji a Jihar Borno.

Harin ya faru ne a daren Juma’a a kusa da kauyen Wajiroko, lokacin da ayarin da Birgediya Janar M. Uba, kwamandan runduna ta 25 ta Task Force Brigade, yake jagoranta ya taso daga sintiri.

Najeriya ta ce shugaban sojojin kasa na raye

Rundunar sojin Najeriya ta fada cewa sojoji hudu sun rasa rayukansu yayin harin kwanton baunan.

Lamarin zai iya zama sabon salo mafi hatsari a yakin ta’addancin da aka shafe shekara 16 ana fafatawa inji masana tsaro.

Sojin Najeriya sun kashe yan Boko Haram 50

Tun da farko sojin Najeriya sun karyata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Janar M. Uba, kuma ya zuwa yanzu ba a kai ga samun wani martani ba daga garesu.