Mayakan jihadi sun kamo hanyar zaman lafiya
February 7, 2019Talla
Fiye da 600 ne suka ajiye makamansu nan take. Mayakan dai sun hada da masu fafutukar jihadi da manyan mambobi na kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai da ayyukansu ya janyo asarar rayuka da dukiya.
Firai ministan Malin, Soumeylou Boubeye Maiga da ya sanar da kaddamar da shirin a watan Disambar bara, ya yaba da matakin ganin yadda suka aka samu hadin kai a tsakanin bangarorin biyu kafin ma cikar wa'adin da gwamnati ta gindaya, ya ce ci gaba ne da zai taimaka ainun a kokarin da ake na samar da tsaro a ciki dama kewayen kasar ta Mali.