Kokarin kwace garin Rakka da ga IS
May 27, 2016![Mayakan Kurdawa na kurdawa cikin garin Rakka](https://static.dw.com/image/19285965_800.webp)
Talla
A cewar kwamandan rundunar mayakan 'yan adawa na Syrian Democratic Forces SDF, kawo yanzu sun kwace kauyuka biyar da kuma wasu yankuna daga hannun IS din a garin na Rakka. Dakarun na SDF dai na taimakawa rundunar taron dangi da Amirka ke wa jagoranci a yakin na Siriya wajen yakar 'yan ta'addan na IS. Nasarar da mayakan na SDF ke samu a Rakka dai na zuwa ne kwana guda da fara kai hare-hare ta sama kan 'yan ta'addan IS din a birnin Fallujah da ke Iraqi.