1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan PKK sun mika makamansu a Iraqi

July 11, 2025

Mayaka kimani talatin na kungiyar PKK mai gwagwarmaya da makamai sun mika makamansu a wani gagarumar bikin da aka gudanar a yankin Kurdistan na kasar Iraqi a wannan Jumma’a.

Hoto: Shwan Mohammed/AFP

Wannan na daga cikin bangaren sulhu da gwamnatin Turkiyya ta yi da mayakan na PKK watanni biyu da suka wuce da ya kawo karshen gwagwarmaya da makamai na kungiyar PKK din na kusan 40 a tsakaninta da gwamnatin Turkiyya.

Masana al'amura sun ce raunana karfin makaman kungiyar ta PKK ya tilasta musu rungumar wannan mataki na sasanci, wanda hakan ya bai wa shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, damar ikirarin samun nasara a kan kungiyar da ke yaki da gwamnatinsatsawon shekaru.

A taron na wannan Juma'a  mayakan 30 na PKK  maza da mata  sanye da kayan sojoji ba tare da rufe fuskokinsu ba sun ce sun mika bindigoginsu da sauran manyan makamai ga gwamnati domin tabbatar da cewa yankin ya samu dawwamamman zaman lafiya. Sun yi hakan a gaban 'yan kallo kimanin 300 wadanda suka fara tafi da hannayensu, suna murna yayin da wasu kuma hawaye ya mamaye fuskokinsu.