Mayakan RFS na Sudan sun halaka mutane 40
November 5, 2025
Hari da mayakan RSF na Sudan suka kai ya hallaka kimanin fararen hula 40 a garin el-Obeid da ke zama helkwatar jihar Arewacin Kordofan, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito. Wannan bayan rahotanni kan irin ta'asa da mayakan na RSF ke aikatawa a yakin da aka kwashe shekaru biyu ana fafatawa.
Lamura sun rincabe
Ofishin jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan Adam ya nuna damuwa kan abin da yake faruwa a Kordofan lokacin da ake ganin ganin yadda makwabtan na Darfur suka shiga mawuyacin hali a hannun mayakan na RSF.
A shekara ta 2023 fada ya barke tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da mayakan rundunar RSF, inda kiyasin hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna kimanin mutane dubu-40 suka mutu a rikicin da ke faruwa, yayin da wasu kimanin milyan 12 suka tsere daga gidajensu, sannan wasu sama da milyan 24 ke fuskantar matsalar karancin abinci.