Mayakan RSF sun kai hari Port Sudan
May 4, 2025
Talla
A karon farko tun bayan barkewar yakin a Sudan a shekarar 2023, mayakan Rapid Support Forces RSF sun kai hari gabashin birnin Port Sudan mai tashohin jiragen ruwa. Kawo yanzu babu rahoton asarar rayuka a harin a cewar kakakin sojin kasar. Sai dai dakarun soji sun tura karin jami'an tsaro zuwa birnin tare da rufe hanyar zuwa fadar shugaban kasa da kuma sansanin sojin kasar.
Karin bayani: Mayakan RSF na ci gaba da halaka 'yan gudun hijira a lardin Darfur
A watannin baya-bayan nan, mayakan RSF na zafafa kai hare-hare zuwa yankunan da ke karkashin ikon sojojin kasar a tsakiya da kuma arewacin kasar. Harin na wannan lahadin na nuna wani gagarumin sauyi a yakin da aka kwashe shekaru biyu ana gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da mayakan RSF.