RSF sun kai hari a masallacin Dafur
October 10, 2025
Hare-haren da dakarun RSF ke kaiwa yankin El-Fasher a baya-bayan na su ne mafi muni tun fara yaki da sojojin gwamnati a watan Afrilun 2023, birnin shi ne babban birni na karshe da ke karkashin ikon sojojin gwamnatin Sudan.
Dakarun RSF sun kai hare-hare tare da mamaye sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke kewaye da birnin, inda rahotanni suka ce sun kashe daruruwan mutane tare da karbar wadanda suka tsira da rayukansu domin tsira.
Mutane 20 sun mutu a harin da RSF ta kai asibitin El-Fasher cikin mako guda, daya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya na karshe da ke aiki a birnin. A watan Agusta, akalla mutane 75 sun mutu a wani harin jirgin yaki mara matuki a wani masallaci.
Rikicin kasar tsakanin bangarorin biyu da ke gwabza yaki kan madafun iko a Sudan, ya yi sanadiyyar miliyoyin mutane sun rabu da gidajensu kazalika kusan 'yan kasar miliyan 25 na cikin matsananciyar yunwa.