Kokarin mayar da Mali hannun farar hula
October 21, 2021Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyan na shirin ziyarar Mali don ganin an mayar da shugabancin kasar a hannun gwamnatin farar hula, a karshen wannnan makon tawagar, za ta isa kasar inda za su tattauna da gwamnatin na yanzu a kokarin shawo kan sojojin da suka kwace mulki don ganin sun mayar da kasar kan tafarkin demokradiyya.
Daya daga cikin wakilan, Abdou Abarry, Jakadan Jamhuriyyar Nijar a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, yankin Sahel na fuskantar matsanancin rashin zaman lafiya ga halin da miliyoyi ke ciki na bukatar taimako a sakamakon aiyukan mayakan jihadi da suka yi kaka gida a yankin Sahel, saboda haka akwai bukatar daukar matakin daidaita kasar kafin samun galaba kan masu tayar da kayar baya.
Kwamitin na fatan ganin sojojin sun bayar da hadin kai, a tsayar da ranar da kasar za ta gudanar da zaben shugaban kasar. Kafin halin da kasar ta tsinci kai a yanzu, Mali da ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a cikin watannin tara, dubbai suka rasa rayukansu wasu daruruwa suka rasa matsuguni a sakamakon tashe-tashen hankula daga aiyukan masu tayar da kayar baya.