1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar kisan da maza ke wa matansu a Ostireliya

July 11, 2023

Sakamakon binciken da gwamnatin Ostireliya ta fitar ya nuna cewa a kowanne kwana 10, mace daya ke mutuwa a hannun wanda ta dauka shi ne mafi kusa da ita wato mijinta.

Hoto: Matthew Childs/REUTERS

Adadin matan da ke mutuwa a hannun mazajensu na cigaba da karuwa a Ostireliya, abin  da ya sa gwamnati neman hanyoyin kara tsaurara dokokin da ke bai wa mata da kananan yara kariya. A ‘yan watannin da suka gabata kadai mata 48 suka hallaka ta wannan hanyar.

Cin zarafin mata da kananan yara babbar matsala ce a Ostireliya wadda ma a yanzu haka annoba ake kiranta. Sashen kula da zamantakewar al’umma ya kaddamar da wani babban shiri na shawo kan matsalar ta hanyar fadakarwa a shekaru 10 masu zuwa wato daga shekarar 2022 zuwa 2023.

Ana kiyasin cewa kowacce mace daya cikin guda uku ta fuskanci cin zarafi daga wurin namiji tun tana da shekaru 15 na haihuwa a yayin da kowace mace daya cikin biyar kuma ta fuskanci fyade.

Sheryn Brown na daga cikin wadanda suka sha da kyar. Bayan da sha wuya a hannun mijinta ta samu ta hada shi da ‘yan sanda inda aka bayar da wata takarda wadda ta ce idan har ya je kusa da ita ko ‘ya’yanta za’a kama shi. Sai dai ta ce wannan takardar bai ba ta irin kariyar da take bukata ba.

Jodie Harrison ita ce ministar da ke kula da cin zarafi tsakanin ma’aurata. Ta ce lallai takardar da ke hana namiji dukan matarsa  na cikin hanoyin da a shekarun baya muke amfani da su amma yanzu dole mu sake daukar matakan da suka fi wannan karfi.

Jodie Harrison ta ce matakan za su dauka yanzu, sun hada da irin takunkumin da ake sanya wa masu sayar da miyagun kwayoyi da ‘yan ta’adda kuma duk wanda aka kama da laifi za’a ci shi tara na dalar Ostireliya dubu 33 kuma zai shafe shekaru biyar a gidan Kasso.

Dokar dai na ci gaba da samun kwaskwarima yayin da matsalar ke karuwa, ko a bara sai da a kara yawan shakarun da mutum zai yi a kurkuku idan har ya rika kokarin azabtar da matarsa.