Bikin ranar masu girki ta duniya
October 20, 2020Talla
Ita dai ranar girkin ta duniya ta samo asali ne daga shekara ta 2004, yayin da aka tabbatar da kwarewar shugabanin iya dafuwa a duniya. To sai dai a bana an fuskanci tarin kalubale na matsalolin da annobar coronavirus ta haifar, wadanda suka shafi fannoni da dama ciki har da shashen dafe-dafen abinci a gidajen sayar da abinci wato restaurant.
Muhawara dai ta barke tsakanin masu yin girkin maza da kuma wadanda ke kiran kansu 'yan gado wato mata a wani gidan sayar da abinci a Jamhuriyar Nijar. A irin wannan rana dai, masu yin girkin na kokarin nuna bajinta da kuma iya girki, kama daga masu yin abincin gargajiya zuwa na zamani na ci gaba da wasa kawunasu.