1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mazauna Zamfara sun hallaka 'yan bindiga 30

Yusuf Ibrahim Jargaba /Ahmed Salisu
October 23, 2026

Rahotanni daga arewa maso yammacin Najeriya na nuni da cewa al’ummar kauyen Birnin Tudu, da ke karamar hukumar Gumi a Jihar Zamfara, sun kashe ’yan bindiga kimanin 30.

Gouverneur des Bundesstaates Zamfara, Dauda Lawal Dare
Hoto: Dauda Lawal/Facebook

Lamarin ya faru ne lokacin da maharan suka kai hari kauyen a kan babura tare da bude wuta, lamarin da ya sa al’ummar kauyen suka fusata tare da afkawa’yan bindigar.

Mustafa Jafaru Kaura, mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Zamfara kan harkokin yada labarai, ya tabbatarwa da DW wannan labari, kuma ya ce mazauna kauyen na cikin shirin ko-ta-kwana.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW