1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAmurka

Mazaunin Washington ya rasu bayan kamuwa da H5N5

Abdullahi Tanko Bala
November 22, 2025

A karon farko wani da ya kamu da cutar murara tsuntsaye nau'in H5N5 wadda ke yaduwa tsakanin mutum da mutum ya rasu. Sai dai jami'an lafiya sun hadarinta ga lafiyar al'umma da sauki.

Gwajin cutar murar tsuntsaye
Hoto: Dado Ruvic/REUTERS

Wani mutum da ake kyautata zato shi ne na farko da ya kamu da murar tsuntsaye nau'in H5N5 da ke yaduwa a tsakanin mutane ya rasu a cewar hukumomin lafiya a Washington na Amurka.

Marigayin ya fito ne daga yankin Grays Harbour kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Washington ta sanar.

Ma'aikatar lafiyar ta ce ba za ta baiyana sunan marigayin da shekarunsa ba domin martaba sirrin iyalansa.