1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mbumba: "Namibiya ta kuduri aniyar yin hadin gwiwa da Jamus"

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
October 9, 2024

Shugaban kasar Namibiya Nangolo Mbumba ya jaddada aniyar hada gwiwa da Jamus wajen samar da makamashi mara gurbata muhalli, don cin moriyar tallafin da kasar ke bai wa kasashen da ta cutar a lokacin mulkin mallaka,

Shugaba Namibia Nangolo Mbumba zai sauka daga karagar mulki bayan Namibiya ta zabi sabon shugaba a babban zabenta na 2024
Shugaba Namibia Nangolo Mbumba zai sauka daga karagar mulki bayan Namibiya ta zabi sabon shugaba a babban zabenta na 2024Hoto: Dirk Heinrich/AP/picture alliance

 

Namibiya na daga cikin kasashen Afirka da ke fama da annobar fari, lamarin da ke zama silar karancin abinci da ke jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin halin 'yunwa da galabaita. Saboda haka ne shugaban kasar ta Namibiya Nangolo Mbumba, wanda ya halarci taron kwanaki biyu da aka gudanar a birnin Hamburg kan al'amuran da suka shafi tallafa wa kasashe masu tasowa, ya ce al'amura sun yi kamari matuka a wannan karo, don haka suka dukufa wajen neman mafita da za ta haifar musu da alhairi.

Karin bayani: Aiwatar da yarjejeniyar Jamus da Namibiya

Mbumba ya ce: ''Tabbas mun shiga dimuwa da rudani sakamakon karancin cimaka, wannan na nuni da irin munin da farin ya yi. Wannan ta sa muka tashi tsaye don ganin mun magance illolin sauyin yanayi da muke fuskanta, ta hanyar amfani da makamashin da ake samarwa daga hasken rana da kuma iska, tunda muna cikin kasashen duniya masu zafi da kuma hamadar sahara, baya ga ruwa da mu ke da shi da kuma kamfanoni, har ma shugaban gwamnatin Jamus ya alkawarta sayen abubuwan da muke samarwa ta wannan fanni. Injiniyoyinmu da masu fasahar tsara taswira sun yi nisa wajen shirin zuwa nan Jamus don samun horon sanin makamar aiki.''.

Karin bayani: Rage amfani da makamashin da ba a sabuntawa

Taron Hamburg ya shaidar da manyan shugabanni da suka yi tattaki zuwa JamusHoto: Georg Wendt/dpa/picture alliance

Wani batu da ya tsaya wa 'yan Namibiya a rai shi ne irin azabatarwa da kuma gallazawar da suka kira kisan kiyashin da suka fuskanta a hannun Jamusawa yayin mulkin mallaka, har ma suke muradin ganin an biya su diyya. Shugaban Namibiya Nangolo Mbumba ya yi tsokaci a kai, inda ya ce "Sai da muka dauki lokaci muna magana da Jamus sannan ta yarda cewa abin da ta aikata kisan kare dangi ne, batun neman afuwa kuma sun ce a shirye suke su nema. Sai kuma hanyoyin bi wajen biyan diyyar rayukan da aka rasa lokacin fafatawa, har ma da wadanda suka mutu a sansanonin da aka killace su. Muna tuntubar juna don samar da masalaha karbabbiya a cikin shekara guda. Za a gudanar da wannan shiri ne mataki mataki don faranta wa al'ummar da muzugunawar ta shafa. Idan an biya kudin diyyar, za mu yi amfani da su wajen sayen filaye da gonaki don mayar wa wadanda suka rasa, tunda kundin tsarin mulkinmu ya ce kada a kwace wa mutum kadara mai rejista ba tare biyan shi diyya ba''. 

Karin bayani: Hulda tsakanin Najeria da Jamus ta karfafa

Gwamnatin Jamus ce ke daukar nauyin gudanar da wannan taro duk shekara, da hadin gwiwar hukumar raya kasashe da kawar da fatara ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP, da nufin bunkasa tattalin arzikin kasashen da ke cikin mawuyacin hali, musamman masu fuskantar matsalolin da sauyin yanayi ke haddasa wa.