MDD: A tsagaita wuta a Ghouta
February 23, 2018Talla
Manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura ya ce lallai ne gwamnatin shugaba Bashar al Assad ta tsagaita wannan tsananin, don bada damar kai akalla kayan agaji da kuma kwashe wadanda hare-haren suka tagayyara. Cikin wata takardar da ya aike wa taron MDD a birnin Geneva, Mr de Mistura, ya ce tilas ne kasashen da suka sanya hannu a taron neman zaman lafiya na birnin Astanan kasar Kazakhstan, su gaggauta zama don sake samar da tuddan mun tsira a Syriar.
Manzon na Majalisar ta Dinkin Duniya, na magana ne 'yan sa'o'i gabanin kuri'ar da kwamitin sulhu zai kada a kan samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30 a Syria.