MDD: Akwai matsala a Zimbabuwe
July 25, 2018Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da yadda rayuwar jama'a ke kara shiga garari a Zimbabuwe, a dai dai lokacin da babban zaben kasar ke kara karatowa.
Zaben da za a yi shi a ranar 30 ga wannan wata na Yuli, shi ne na farko bayan murabus na tsohon Shugaba Robert Mugabe da ya mulki kasar na tsawon shekaru 37.
Shugaba Emmerson Mnangagwa mai mulki dai ya yi alkawarin samar da sahihin zabe, sai dai ga alama, ya kama hanyar saba alkawarin da ya yi.
Hukumar kula da kuma kare hakkin bil Adama ta Majlisar Dinkin Duniyar, ta ce tana samun rahotannin yawaitar fitintinu da kuma muzguna wa jama'a musamman a yankunan karkara.