Katsalandn daga ketare a Libiya
July 9, 2020Talla
Babban sakataren ya kara da cewar a halin da ake ciki yanzu, wakilan majalisar na can a kasar ta Libiya suna kokarin ganin an cimma tsagaita wuta tsakanin dakarun da ke fada domin cetar da rayukan alumma.
Guterres ya ce daga farkon watan Afirilu zuwa karshen watan Yuni an kashe sama da fararen huda dari tare da jikkata sama da dari biyu da hamsin, wanda sakataren ya ce na zama sama da kaso 170 idan aka kwatanta da kwatan farko na wannan shekarar.