Tashar nukiliya a Zaporizhzhia na cikin hadari
September 7, 2022Talla
Sojojin Rasha sun kwace iko da tashar nukiliyar da ke zama mafi girma a nahiyar Turai.
A watan Maris an kai farmaki sau da dama kusa da tashar nukiliyar, lamarin da ya haifar da fargabar aukuwar mummunan bala'i na makamashin nukiliya.
Jm'ian hukumar makamashin nukiliya ta majalisar Dinkin Duniya IAEA sun ce halin da ake ciki yanzu a tashar nukiliyar bai dace ba.
Hukumar ta ce akwai bukatar gaggawa ta samar da wani shiri na wucin gadi domin kare aukuwar hadari a tashar nukiliyar.
A yayin taron Majalisar Dinkin Duniya Rasha ta ce abin takaici ne kwarai rahoton bai zargi Ukraine da kai hari kusa da tashar nukiliyar ba.