1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude babban taron MDD ta hanyar bidiyo

September 22, 2020

An kaddamar babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi nashekara-shekara. Taron da ke samun halartar shugabannin kasashe sama da 100, na guda ne ta bidiyo.

USA, New York I 75. Jahrestag der Vereinten Nationen
Hoto: Eskinder Debebe/United Nations /AP/picture-alliance

Sai dai a wannan shekarar sabanin shekarun baya akasarin shugabannin duniya za su halarci taron ta hanyar bidiyo a maimakon taron gaba-da-gaba da ake yi a birnin New York a saboda corona. 

Shugabannin kasashe daban-daban za su mayar da hankali kan yadda za a magance cutar corona. To amma jawabin Shugaba Donald Trump na Amirka shi ne zai fi daukar hankali musamman kan rikicin da ke a tsakaninsa da Iran.