1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Idai ta yi barna a kudancin Afirka

Abdullahi Tanko Bala
March 20, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mahaukaciyar guguwar Idai wadda ta fada kudancin Afirka, ta kasance mafi muni da ta afkawa yankin, da kuma ta haifar da tagaiyarar al'umma a kasashen Malawi da Mozambique da kuma Zimbabuwe

Rettungseinsätze nach Wirbelsturm «Idai»
Mutane na tono 'yan uwansu da laka ta rufe su.Hoto: picture-alliance/AP/T. Mukwazhi

Kiyasi ya nuna cewa a kasar Malawi kadai guguwar ta shafi mutane kimanin miliyan daya tare kuma da raba mutane 80,000 da muhallansu. Bugu da kari guguwar hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi mummunan ta'adi a kasar Mozambique inda ta yaye rufin gidaje da haddasa ambaliyar ruwa. kayan abinci sun fara isa sannu a hankali ga mutanen da guguwar ta tagaiyara sai dai ruwan sama da ake cigaba da yi na kawo tsaiko ga aikin agajin.

 

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef ta ce dubban mutane da suka hada da yara kanana na cikin mawuyacin hali. A kasashen Mozambique da Malawi da kuma Zimbabuwe ruwa ya yi awon gaba da gadoji da katse hanyoyi.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta yi kiyasin cewa mutane kimanin 400,000 sun rasa muhallansu.