1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin mutane zai kai biliyan 8

Abdul-raheem Hassan
July 11, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen yawan al'ummar duniya zai kai biliyan Takwas a tsakiyar watan Nuwamban 2023, a karon farko kasar Indiya za ta zarta China a yawan mutane a duniya nan da 2023 a cewar rahoton.

Bangladesch Corona-Pandemie Shimulia Fähre
Hoto: Mahmud Zaman Ove/bdnews24

Hasashen da Ma'aikatar Tattalin Arziki da Zamantakewa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi, ya ce yawan al'ummar duniya na karuwa a cikin sauri tun a shekara ta 1950. Ana hasashen samun yawan bil adama biliyan 8 da miliyan 500 a shekarar 2030 sannan adadin zai karu zuwa biliyan 9 da miliyan 700 a shekarar 2050.

Rahoton ya ce yayin da ake samun raguwar haihuwa a kasashe masu tasowa da dama, fiye da rabin hasashen karuwar al'ummar duniya a cikin shekaru masu zuwa zai ta'allaka ne a kasashe takwas, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da  Masar da Habasha da Indiya da Najeriya da Pakistan da Philippines da kuma Tanzaniya.