MDD: Jama'a na fama da yunwa a Tigray
June 11, 2021Talla
Kungiyoyin agaji sun dora alhakin halin da aka shiga na yunwa a yankin Tigray akan rikicin baya bayan nan da ya barke a yankin.
Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya yace sama da mutum miliyan biyar na bukatar tallafin abinci.
Kungiyoyin agaji sun ce halin da ake ciki a yankin na Tigray shi ne mafi muni da aka gani tun bayan annobar fari da ta auku a Somalia a shekarun 2010 zuwa 2012 da ta hallaka yan Somalia fiye da dubu 250 yawancin su kananan yara.
Wani babban jami'in kungiyar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya Luca Russo yace yunwar ta yi tsanani kuma mutane na mutuwa musamman yara kanana wadanda basa samun abin da za su ci.