1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Mutane 606 sun bace a Bahar Maliya

February 23, 2026

Rahoton Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa, a kalla bakin haure 606 ne suka mutu ko suka bace a tekun Bahar Maliya a shekarar 2026.

Jirgi dauke da wasu bakin haure da aka ceto a Crete yayin da suke kokarin dosar Girka
Jirgi dauke da wasu bakin haure da aka ceto a Crete yayin da suke kokarin dosar GirkaHoto: Costas Baltas/Anadolu Agency/IMAGO

Wannan shi ne rahoto mafi muni da aka samu a farkon shekara a Bahar Maliyar tun bayan da Hukumar kula kaurar jama'a ta duniya ta fara daukar alkalumma a shekarar 2014. Wani kakakin hukumar na cewa, a kalla mutane 30 ne suka yi batan dabo bayan da kwale-kwalensu da ya doshi Girka ya kife a wannan Asabar din. Yawancin fasinjojin kananan yara ne 'yan kasashen Sudan da Masar.

Ko a shekarar da ta gabata an ci gaba da ganin kwarar bakin haure daga kasar Libiya a wani mummunan yunkuri na isa Girka da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Hukumar ta IOM ta yi kira da a kara hadin gwiwa a yankin tare da karfafa ayyukan bincike da ceto a tsakiyar tekun sakamakon cin zarafin da masu safarar mutane ke yi.

 

       

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW