MDD: Mutane na fama da matsala a Yemen
May 10, 2017Talla
Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a lardin Taez na Yemen Shabiya Mantoo, ya ce daruruwan mutane ne suka rasa muhallinsu kuma ke fama da karancin abinci, duk da cewa rikici bai kazanta ba a kasar, kuma galibinsu a yankin Hudeida ne.
A cewar jami'in a halin da ake ciki akwai mata da kananan yara masu yawa da ke barar abin da za su ci a manyan tituna, sakamakon yawan jama'ar da ta yiwo hijira shekaru biyun da suka gabata.
Akalla rayuka mutam dubu 7 da 700 ne suka salwanta yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhalli, sakamakon rikici a Yemen a shekara ta 2015.